價格:免費
更新日期:2018-10-21
檔案大小:1.9M
目前版本:1.0
版本需求:Android 2.3.3 以上版本
官方網站:http://www.kamus.com.ng
Email:admin@shamsuddeen.com
聯絡地址:Zaria, Kaduna State Nigeria
1. Ko kun san Annobar yunwa mafi muni da aka taɓa yi a tarihin duniya ita ce wacce aka yi a shekara ta 1932 zuwa 1933 a ƙasar Sin (China) inda mutane sama da miliyan arba'in suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan bala'in yunwar.
2. Ko kun san Yaƙi mafi muni da aka taɓa yi a tarihin Nigeria shine yaƙin basasar shekara ta 1967, wato yaƙin biafra, lokacin da iyamurai suka ayyana ɓallewa daga Nigeria. Kimanin mutane miliyan ɗaya suka rasa rayukansu sanadiyyar wannan yaƙin.
3. Jihar Kano itace jiha mafi yawan jama'a a Nigeria.
4. Lalacewar ƙwaƙwalwa zai iya aukuwa ne kawai idan zafin zazzaɓi ya kai 107.6° farenheit.
5. An yi dashen zuciya na farko ne a 3 Dec 1967.
6. Tururuwa basa yin barci.
7. Baza ka iya kashe kanka ta hanyar riƙe nunfashinka ba.
8. Cakuleti zai iya kashe karnuka, domin ya ƙunshi sinadarin theobromine wanda yake shafan zuciyoyinsu da jijiyoyi.
9. Dodon koƙi zai iya yin barcin shekaru uku.
10. Zuma ce kawai abincin da baya lalacewa.
11. Idanun jarirai ba za su iya yin hawaye ba har sai sun kai makonni shida zuwa takwas a duniya.
12. Nigeria wacce take da yaruka 521, itace ta huɗu a yawan yaruka a duniya.
13. Turawan ƙasar Portugal sun iso Nigeria a shekara ta 1472.
14. A shekara ta 1880 Turawan Birtaniya suka fara mamaye kudancin Nigeria, amma sai a shekara ta 1903 suka fara mamaye arewacin Nigeria.
Domin sanin waɗannan bayanan dama wasu sauran ɗaruruwan bayanai sai ka saukar da wannan manhajar.